Friday, March 29, 2019

mimbarin sunnah




*Tambaya*

Assalamu alaikum, shin ya halatta Arniyya ta yiwa musulma Kitso ?

*Amsa*

Wa'alaikumus salam
Ya halatta macen da ba musulma  ba ta yiwa musulma kitso, saboda a zancen mafi inganci, al'aurar mace ga 'yar'uwarta mace, shi ne daga guiwa zuwa cibiya, babu bambanci tsakanin kafira da musulma a cikin haka, domin a zamanin Annabi s.a.w. Yahudawa mata suna shiga gidan Annabi s.a.w., kuma ba'a samu suna yin shiga ta musamman ba idan suka ga za su shigo, saidai in kafirar tana da wani sharri da ake jin tsoro, to wannan mace za ta iya suturta daga ita, sannan kuma mutukar akwai musulma to ita ta fi dacewa ayi hulda da ita .

ALLAH NE MA FI SANI

*Dr. Jamilu Yusuf Zarewa*





*Tambaya*

Assalamu alaikum.malam mutum ne ya rasu ya bar mata daya bai taba haihuwa ba, kuma iyayen shi duk sun rasu, sai kannan shi maza da mata wadanda suke uwa daya uba daya da kuma wadanda suke uba daya kawai, yaya rabon gadon zai kasance?

*Amsa*

Wa alaikum assalam, Za'a raba abin da ya bari gida hudu, a bawa matarsa kashi daya, ragowar sai a bawa 'yan'uwansa wadanda suke uwa daya uba daya su raba, duk namiji ya dau rabon mata biyu.

'Yan uba ba sa gado mutukar akwai namiji shakiki.

Allah ne mafi sani

*Dr. Jamilu Zarewa*




*Tambaya*

Assalamu Alaykum wa rahamatullahi wa barakatuhu. Da fatan mallam da duka jama'ar wannan fili na cikin ƙoshin lafiya. Tambaya ta, mallam, ita ce, mutum ne ya ke bacci, ya na cikin baccin nan har lokacin sallah ya yi, shin za'a tashe shi ne daga baccin ya yi sallah? Ko kuwa barin shi za'a yi har sai lokacin da ya tashi da kan shi, sannan ya yi ramuwar sallah?

*Amsa*

Wa alaikum assalam
Za'a tashe shi mana, in har ba lalura ce da shi ba, da zai cutu in ya farka, saboda a taimaka masa wajan aikata Alkairi, da yin sallah a lokacinta.

Allah ya umarci Muminai da taimakekeniya wajan biyayya ga Allah a aya ta (2) a suratul Ma'idah.
Annabi SAW a cikin hadisin Abu-dawud ya yi adduar Rahma ga mutumin da ya ta shi da daddare don ya yi sallah ya ta shi matarsa, in ba ta tashi ba ya yayyafa mata ruwa.
In har bai samu wanda zai tashe shi ba, ya yi sallah bayan lokacinta ya wuce, to Allah ya dauke Alkalami akansa kamar yadda ya zo a hadisi tabbatacce.

Allah ne mafi sani

*Amsawa*✍🏻

*DR. JAMILU YUSUF ZAREWA*

Sabbin Karatu

3/recent-posts
Shugaban mimbarin sunnah

Yahuza Tahir Abu Albany

Wannan shafine da zamu rinka kawo muku karatuttukan malaman sunnah.